5
Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa. Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa. Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane. Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu. Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne. Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini. Domin akwai uku wadanda suke bada shaida: Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce. Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa. 10 Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba. 11 Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa. 12 Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai. 13 Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami—a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah. 14 Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu. 15 Haka kuma, in mun san yana jinmu—Duk abin da mu ka rokeshi—mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi. 16 Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17 Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba. 18 Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba. 19 Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan. 20 Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada. 21 'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.