3
Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna. Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya. Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu. Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani. Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza. Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku. Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu. Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji. Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku? 10 Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku. 11 Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku. 12 Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku. 13 Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.