6
1 'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji.
2 Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu.
3 Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi.
4 Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba.
5 Domin kowa zai dauki nauyin kayansa.
6 Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa.
7 Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba.
8 Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu.
9 Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba.
10 Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya.
11 Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna.
12 Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu.
13 Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku.
14 Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya.
15 Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci.
16 Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah.
17 Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina.
18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.