Kolosiyawa
1
1 Bulus manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah da Timoti dan'uwanmu,
2 zuwa ga masu bada gaskiya da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Bari alheri da salama su kasance tare da ku daga wurin Allah Ubanmu.
3 Muna godiya ga Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kuma kullum muna addu'a dominku.
4 Mun ji bangaskiyar ku cikin Almasihu Yesu da kaunar da kuke da ita wa dukan kebabbu ga Allah.
5 Kuna da kaunar nan domin bege na hakika ga abin da aka tanadar maku a sama. Kun riga kun ji game da begen nan na hakika maganar gaskiya da bishara,
6 wanda ta zo maku. Wannan bishara tana ba da yaya tana kuma hayayyafa da kuma girma a cikin dukan duniya. Tana yin haka a cikinku kuma tun ranar da kuka ji ta kun kuma yi koyi game da alherin Allah cikin gaskiya.
7 Wannan itace bishara kamar yadda kuka koye ta a wurin Abafaras, kaunataccen abokin bautar mu, wanda ke amintacce mai hidimar Almasihu a madadin mu.
8 Abafaras ya bayyana mana kaunarku a Ruhu.
9 Saboda da wannan kauna, tun daga ranar da muka ji haka, ba mu fasa yi maku addu'a ba. Muna ta roko domin ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima da fahimta ta ruhaniya.
10 Muna ta addu'a domin ku yi tafiya da ta cancanci Ubangiji a kowace hanya da za ta faranta masa rai. Muna ta addu'a cewa za ku ba da 'ya'ya cikin kowanne aikin nagari kuma za ku yi girma cikin sanin Allah.
11 Muna addu'a ku karfafa a cikin kowanne iyawa bisa ga ikon daukakarsa zuwa ga matukar jimrewa da hakuri.
12 Muna addu'a za ku yi godiyar farinciki ga Uban, wanda ya sa kuka samu rabo cikin gado na masu bangaskiya cikin haske.
13 Ya kwato mu daga mulkin duhu ya kuma maishe mu ga mulkin kaunataccen Dansa.
14 Ta wurin Dan ne muka sami fansa, gafarar zunubai.
15 Dan shine surar Allah mara ganuwa. Shine farkon dukan hallitta.
16 Domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, wadanda ke sama da wadanda ke duniya, masu ganuwa da marasa ganuwa. Ko kursiyai ko mulkoki ko sarautai ko ikoki, dukan abubuwa shi ya hallice su kuma dominsa.
17 Ya kasance kafin dukan abubuwa, a cikinsa ne kuma komai yake hade.
18 Kuma shine kan jikin, ikilisiya. Shine farko da kuma dan fari daga cikin matattu, don haka yana da wuri na fari a cikin dukan abubuwa.
19 Domin Allah ya yi farinciki cewa dukan cikarsa ta kasance a cikinsa,
20 kuma ya sulhunta kowanne abu zuwa gare shi ta wurin Dan. Allah ya kawo salama ta wurin jinin giciyensa. Allah ya sulhunta duka zuwa gare shi, ko abubuwan da ke duniya ko abubuwan da ke sama.
21 Domin a da ku baki ne ga Allah, kuma makiyansa ne cikin zuciya da cikin mugun ayyuka.
22 Amma yanzu, ya sulhunta ku ta wurin mutuwarsa ta jiki. Ya yi haka domin ya mika ku tsarkakaku, marasa aibu da marasa abin zargi a gabansa,
23 idan kuka ci gaba cikin bangaskiya, kafaffu da tsayayyu, marasa kaucewa daga begen ku na hakika na bishara da kuka ji. Wannan itace bishara da aka yi wa kowanne halitaccen taliki a karkashin sama. Wannan itace bishara wadda ni, Bulus, na zama bawa.
24 Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya.
25 Saboda wannan ikilisiya na zama bawa, bisa ga haki da Allah ya ba ni domin ku, domin cika sakon Allah.
26 Wannan shine asirin gaskiya da yake a boye shekara da shekaru da zamanai. Amma a yanzu an bayyana shi ga wadanda suka gaskanta da shi.
27 A gare su ne Allah ya so ya bayyana yalwar daukakar asirin gaskiyarsa a tsakanin al'ummai. Ya nuna Almasihu ne ke cikin ku, tabbacin daukaka mai zuwa.
28 Wannan shine wanda muke shella. Muna gargadar da kowanne mutum, muna kuma koyar da kowanne mutum tare da dukan hikima, don mu mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu.
29 Domin wannan nake aiki da himma bisa ga karfinsa da yake aiki a cikina da iko.