2 Korantiyawa
1
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma Timoti dan'uwan mu, zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Korantus, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya.
2 Bari alheri ya kasance tare da ku da kuma salama ta Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
3 Bari yabo ya tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine Uba na dukan jiyejiyenkai, da kuma Allah na dukan ta'aziya.
4 Allah yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da wadanda ke cikin kowace wahala. Muna ta'azantar da wasu da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu.
5 Gama kamar yadda wahalhalun Almasihu suka karu domin mu, haka kuma ta'aziyarmu ta yawaita cikin Almasihu.
6 Amma fa idan muna shan wuya, domin ta'aziyarku ne da cetonku. Haka kuma in mun ta'azantu, domin ta'aziyarku ne. Ta'aziyarku tana aiki ne sosai yayinda kuka jure da irin shan wuyar da mu ma muke sha.
7 Kuma gabagadinmu game da ku tabbatacce ne. Mun kuwa sani kamar yadda kuke tarayya cikin shan wahalhalun, haka kuma za ku yi tarayya cikin ta'aziyyar.
8 Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu.
9 Hakika, mun ji hukuncin mutuwa akan mu. Amma wannan ya faru ne domin kada mu dogara ga kanmu, sai dai ga Allah, wanda ke tada matattu.
10 Ya kubutar da mu daga wannan mummunan hatsari na mutuwa, kuma zai sake kubutar da mu. Mun kafa begenmu gare shi cewa zai sake kubutar da mu.
11 Zai aikata wannan yayinda kuka taimake mu da addu'ar ku. Sa'an nan da dama za su bada godiya a madadin mu don tagomashin alheri da aka yi mana ta wurin addu'o'in mutane masu yawa.
12 Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah.
13 Bamu rubuta maku abinda ba za ku iya karantawa ko fahimta ba. Ina fata za ku fahimce mu baki daya,
14 kamar yadda kuka fahimce mu kadan yanzu. Daganan a ranar Ubangijinmu Yesu za mu zama dalilinku na alfahari, kamar yadda za ku zama namu.
15 Saboda gabagadin da nake da shi game da haka, naso in zo gare ku da farko, domin ku amfana da ziyara sau biyu.
16 Ina da shirin ziyaratar ku a kan hanyata ta zuwa Makidoniya. Daga nan kuma ina da yi niyyar in sake ziyartar ku, a tafiya ta daga Makidoniya, domin ku aike ni a hanyata ta zuwa Yahudiya.
17 Yayinda nake irin wannan tunani, ina shakka ne? Ina shirya abubuwa ne bisa ga magwajin mutum, ta yadda har zan ce “I, i” da “A, a, a, a” a lokaci guda?
18 Amma kamar yadda Allah yake amintacce, ba ma fadin ''I'' da ''A'a'' a lokaci guda.
19 Gama Dan Allah, Yesu Almasihu, wanda Silbanus da Sila, da Ni muka shaida maku, ba “I” da “A, a” ba ne. Maimakon haka, Shi “I” ne a kodayaushe.
20 Gama dukan alkawaran Allah 'I' ne a cikin sa. Haka kuma ta wurin sa muna cewa ''Amin'' zuwa ga daukakar Allah.
21 Yanzu dai Allah ne ya tabbatar da mu da ku a cikin Almasihu, ya kuma kebe mu.
22 Ya sa hatiminsa a kan mu ya kuma ba mu Ruhu a zuciyar mu a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya.
23 Maimakon haka, na yi kira ga Allah ya zama shaida domina, cewa dalilin dayasa banzo Korintis ba domin in kare ku ne.
24 Ba muna kokarin mu sarrafa yadda bangaskiyar ku za ta zama ba ne. Maimakon haka, muna aiki tare da ku ne domin farincikinku, yayinda kuke tsaye cikin bangaskiyarku.