6
1 A wadannan kwanaki, yawan almajiran ya ci gaba da ribanbanya, sai Yahudawan da suke zama a kasar Helanawa suka fara gunaguni game da Yahudawan Isra'ila, domin basu damu da gwamrayensu, wajen raba abinci da ake yi kullum.
2 Manzannin nan sha biyu suka kira taron almajiran suka ce masu, ''Bai kamata mu bar maganar Allah mu shiga hidimar rabon abinci ba.
3 Don haka ku zabi 'yan'uwa maza daga cikinku, mutane bakwai wadanda a ke ganin su da daraja, cike da Ruhu da kuma hikima, wadanda za mu zaba suyi wannan hidima.
4 Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar.''
5 Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci.
6 Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu.
7 Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya.
8 Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a.
9 Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus.
10 Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi.
11 Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, ''Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah.''
12 Sai suka zuga mutanen, har da dattawa da marubuta suka tunkari Istifanus, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa.
13 Suka kawo masu shaidar karya suka ce, ''Wannan mutumin har yanzu bai dena maganganun gaba akan wannan wuri mai tsarki da kuma shari'a ba.
14 Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa.''
15 Dukan wadanda suke zaune a majalisar suka zuba masa ido, sai suka ga fuskarsa kamar ta mala'ika.