15
1 Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, “Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba.”
2 Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana.
3 Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa.
4 Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu.
5 Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, “Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa.”
6 Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari.
7 Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, “'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya.
8 Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana;
9 kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya.
10 To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba?
11 Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke.”
12 Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai.
13 Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, “'Yan'uwa, ku ji ni.
14 Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa.
15 Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce,
16 'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi,
17 saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana.
18 Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da.
19 Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah;
20 amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe.
21 Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci.”
22 Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba.
23 Sai suka rubuta wasika, “Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa.
24 Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali.
25 Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba,
26 mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu.
27 Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa.
28 Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan:
29 ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya.”
30 Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar.
31 Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa.
32 Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa.
33 Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su.
34 Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin.
35 Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji.
36 Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, “Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke.
37 Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus.
38 Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba.
39 Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus.
40 Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su.
41 Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.