13
1 A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu.
2 Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su”.
3 Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su.
4 Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus.
5 Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu.
6 Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya.
7 Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah.
8 Amma Elimas “mai tsafi” (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya.
9 Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido.
10 Sai ya ce, “Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba?
11 Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci.” Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora.
12 Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji.
13 Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima.
14 Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna.
15 Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, “'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi.”
16 Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, “Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji.
17 Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta.
18 Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in.
19 Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado.
20 Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo.
21 Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in.
22 Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'.
23 Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi.
24 Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila.
25 Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.'
26 Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto.
27 Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi.
28 Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi.
29 Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu.
32 Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu.
33 Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: ''Kai da na ne yau na zama mahaifinka.''
34 Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: ''Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu.''
35 Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.'
36 Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba,
37 amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba.
38 'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai.
39 Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba.
40 Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku:
41 'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku.”
42 Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa.
43 Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah.
44 Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji.
45 Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi.
46 Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, “Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai.
47 Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'”
48 Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba.
49 Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin.
50 Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu.
51 Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya.
52 Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.