13
Tsarkakewa daga zunubi
“A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta.
“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar. In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi.
“A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu. Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’* In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’
An bugi makiyayin, tumakin suka watse
“Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina,
mutumin da yake kusa da ni sosai!”
In ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Kashe makiyayin,
sai tumakin su watse,
in kuma tayar wa ƙananan.
A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji,
“kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka;
duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta.
Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta;
zan tace su kamar azurfa
in gwada su kamar zinariya.
Za su kira bisa sunana
zan kuwa amsa musu;
zan ce, ‘Su mutanena ne,’
za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”
* 13:5 Ko kuwa manomi; wani mutum ya sayar da a ƙuruciyata 13:6 Ko kuwa miyaku a tsakanin hannuwanka