11
1 Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon,
don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.
2 Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi;
itatuwa masu daraja sun lalace!
Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan;
an sassare itatuwan babban kurmi!
3 Ku ji kukan makiyaya;
an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi!
Ku ji rurin zakoki;
an lalatar da jejin Urdun!
Makiyaya biyu
4 Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka.
5 Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.
6 Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”
7 Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken.
8 Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku.
Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su
9 na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”
10 Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai.
11 An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.
12 Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.
13 Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
14 Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila.
15 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi.
16 Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu.
17 “Kaito ga banzan makiyayin nan,
wanda ya bar garken!
Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama!
Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf,
idonsa na dama kuma yă makance sarai!”