5
Akwatin alkawari a Ashdod da Ekron
1 Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod.
2 Sa’an nan suka ɗauki akwatin alkawarin suka kai shi cikin haikalin gunkinsu Dagon, suka ajiye kusa da Dagon.
3 Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.
4 Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.
5 Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau.
6 Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai.
7 Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.”
8 Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?”
Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.
9 Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro.
10 Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron.
Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, “An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin yă kashe mu da mutanenmu.”
11 Saboda haka suka kira ga dukan shugabannin Filistiyawa suka ce, “Ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila inda ya fito; in ba haka ba zai kashe mu da mutanenmu.” Gama mutuwa ta cika garin da tsoro. Hannun Allah ya yi nauyi a kansa.
12 Waɗanda ba su mutu ba kuwa, sun kamu da marurai. Kukan birnin kuwa ta hau har zuwa sama.