9
Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu.
Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. 10 Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. 11 Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon.*
12 Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
13 Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. 14 Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” 15 Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. 16 Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
17 Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. 18 Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. 19 Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
20 Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. 21 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
* 9:11 Abaddon da kuma Afolliyon suna nufin Maihallakarwa.