17
Babilon, karuwa a kan dabbar
Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”
Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne,
Babilon mai girma
mahaifiyar karuwai
da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya.
Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu.
Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.
“Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. 10 Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. 11 Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta.
12 “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. 13 Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu. 14 Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.”
15 Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. 16 Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. 17 Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. 18 Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”