Zabura 64
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna;
ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.
 
Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,
daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.
Sukan wāsa harsunansu kamar takuba
su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa.
Sukan yin kwanto su harbi marar laifi;
sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro.
 
Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu,
sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu;
su ce, “Wa zai gan su?”*
Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce,
“Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!”
Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa.
 
Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi;
nan da nan za a buge su su fāɗi.
Zai juya harshensu a kansu
yă kuma kawo su ga hallaka;
duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.
Dukan mutane za su ji tsoro;
za su yi shelar ayyukan Allah
su kuma yi tunanin abin da ya aikata.
 
10 Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji
su kuma nemi mafaka a gare shi;
bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!
* Zabura 64:5 Ko kuwa mu