Zabura 57
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. 
 
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,  
gama a gare ka raina yake samun mafaka.  
Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka  
sai masifar ta wuce.   
   
 
2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka,  
ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.   
3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni,  
yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; 
Sela
  
Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.   
   
 
4 Ina tsakiyar zakoki;  
ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane,  
mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi,  
waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.   
   
 
5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;  
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.   
   
 
6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna,  
damuwa ta sha ƙarfina.  
Sun haƙa rami a hanyata,  
amma su kansu suka fāɗa a cikinta. 
Sela
   
   
 
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,  
zuciyata tana nan daram;  
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.   
8 Ka farka, raina!  
Ku farka, garaya da molo!  
Zan sa safe yă farka.   
   
 
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;  
zan rera game da kai a cikin mutane.   
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;  
amincinka na kaiwa sarari.   
   
 
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;  
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.