Zabura 52
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.”
1 Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?
Me ya sa kake fariya dukan yini,
kai da kake abin kunya a idanun Allah?
2 Harshenka kan shirya hallaka;
yana nan kamar reza mai ci,
kana ta ruɗu.
3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,
ƙarya a maimakon faɗin gaskiya.
Sela
4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,
Ya kai harshe mai ruɗu!
5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.
Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;
zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai.
Sela
6 Masu adalci za su ga su ji tsoro;
za su yi masa dariya, suna cewa,
7 “Yanzu, ga mutumin
da bai mai da Allah mafakarsa ba
amma ya dogara a yawan arzikinsa
ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
8 Amma ni kamar itace zaitun ne
ina haɓaka a gidan Allah;
na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah
har abada abadin.
9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;
a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.
Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.