Zabura 48
Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza.
1 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo,
a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
2 Kyakkyawa ce cikin tsayinta,
abin farin cikin dukan duniya.
Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona,
birnin Babban Sarki.
3 Allah yana cikin fadodinta;
ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
4 Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni,
sa’ad da suka yi gaba tare,
5 sun gan ta suka kuwa yi mamaki;
suka gudu don tsoro.
6 Rawar jiki ya kama su a can,
zafi kamar na mace mai naƙuda.
7 Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish
da iskar gabas ta wargaje.
8 Yadda muka ji,
haka muka gani
a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,
a cikin birnin Allahnmu.
Allah ya sa ta zauna lafiya
har abada.
Sela
9 Cikin haikalinka, ya Allah,
mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
10 Kamar sunanka, ya Allah,
yabonka ya kai iyakokin duniya;
hannunka na dama ya cika da adalci.
11 Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki,
ƙauyukan Yahuda suna murna
saboda hukuntanka.
12 Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta,
ku ƙirga hasumiyoyinta,
13 ku lura da katangarta da kyau,
ku dubi fadodinta,
don ku faɗe su
ga tsara mai zuwa.
14 Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin;
zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.