Zabura 46
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza
duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa
duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu.
Sela
4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna,
tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba;
Allah zai taimake ta da safe.
6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi;
ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;
Allah na Yaƙub ne kagararmu.
Sela
8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji,
kangon da ya kawo a kan duniya.
9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit
ko’ina a duniya.
Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,
ya ƙone garkuwoyi da wuta.
10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;
za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,
za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;
Allah na Yaƙub ne kagararmu.
Sela