Zabura 3
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. 
 
1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!  
Su nawa suke gāba da ni!   
2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa,  
“Allah ba zai cece shi ba.” 
Sela
   
   
 
3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;  
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.   
4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,  
ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. 
Sela
   
   
 
5 Na kwanta na yi barci;  
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.   
6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma  
suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.   
   
 
7 Ka tashi Ya Ubangiji!  
Ka cece ni, ya Allahna!  
Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;  
ka kakkarya haƙoran mugaye.   
   
 
8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.  
Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. 
Sela