Zabura 29
Zabura ta Dawuda. 
 
1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,  
ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.   
2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;  
ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.   
   
 
3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;  
Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,  
Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.   
4 Muryar Ubangiji mai iko ce;  
muryar Ubangiji da girma take.   
5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.  
Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.   
6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi,  
Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.   
7 Muryar Ubangiji ta buga  
da walƙatar walƙiya.   
8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada  
Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.   
9 Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak  
ya kakkaɓe itatuwan kurmi.  
Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”   
   
 
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;  
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.   
11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;  
Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.