Zabura 15
Zabura ta Dawuda. 
 
1 Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?  
Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?   
   
 
2 Sai wanda ba shi da laifi  
kuma yana yin abin da yake daidai,  
wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa   
3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,  
wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta  
ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,   
4 wanda yake ƙin mugun mutum  
amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,  
yakan cika alkawarinsa  
ko da ma ya zafe shi,   
5 wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba  
kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.  
   
 
Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa  
ba zai taɓa jijjiguwa ba.