Zabura 147
1 Yabi Ubangiji.
Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,
abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
2 Ubangiji ya gina Urushalima;
ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
3 Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
4 Ya lissafta yawan taurari
ya kuma kira kowannensu da suna.
5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;
ganewarsa ba shi da iyaka.
6 Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai
yakan yar da mugaye a ƙasa.
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
9 Yakan tanada wa shanu abinci
da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
10 Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki,
balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;
11 Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa,
waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
12 Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima;
ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.
13 Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki
yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
14 Yana ba da salama ga iyakokinki
yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
15 Yana ba da umarninsa ga duniya;
maganarsa tana tafiya da sauri.
16 Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu
yă kuma watsar da hazo kamar toka.
17 Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu.
Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?
18 Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su;
yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.
19 Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub,
dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.
20 Bai yi wannan ga wata al’umma ba;
ba su san dokokinsa ba.
Yabi Ubangiji.