Zabura 138
Ta Dawuda. 
 
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;  
a gaban “alloli” zan rera yabo.   
2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki  
zan kuma yabi sunanka  
saboda ƙaunarka da amincinka,  
saboda ka ɗaukaka a bisa kome  
sunanka da kuma maganarka.   
3 Sa’ad da na kira, ka amsa mini;  
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.   
   
 
4 Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,  
sa’ad da suka ji maganganun bakinka.   
5 Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,  
gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.   
   
 
6 Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu,  
amma tun da nesa ya san masu girman kai.   
7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,  
kana kiyaye raina;  
ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,  
da hannunka na dama ka cece ni.   
8 Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;  
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,  
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.