Zabura 121
Waƙar haurawa. 
 
1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,  
ta ina ne taimakona zai zo?   
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,  
wanda ya kafa sama da ƙasa.   
   
 
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,  
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;   
4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila  
ba ya gyangyaɗi ko barci.   
   
 
5 Ubangiji yana tsaronka,  
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;   
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba  
balle wata da dare.   
   
 
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,  
zai tsare ranka;   
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka  
yanzu da har abada kuma.