Zabura 114
1 Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar,  
gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,   
2 Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah,  
Isra’ila mallakarsa.   
   
 
3 Teku ya kalla ya kuma gudu,  
Urdun ya juye da baya;   
4 duwatsu suka yi tsalle kamar raguna,  
tuddai kamar tumaki.   
   
 
5 Me ya sa, ya teku, kika gudu,  
Ya Urdun, ka juya baya,   
6 ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna,  
ku tuddai, kamar tumaki?   
   
 
7 Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji,  
a gaban Allah na Yaƙub,   
8 wanda ya juye dutse ya zama tafki,  
dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.