Zabura   
LITTAFI NA ƊAYA  
 1
Zabura 1–41  
1 Mai farin ciki ne mutumin  
da ba ya aiki da shawarar mugaye  
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi  
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.   
2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,  
kuma yana ta nazarinta dare da rana.   
3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,  
wanda yake ba da amfani a daidai lokaci  
wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.  
Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.   
   
 
4 Ba haka yake da mugaye ba!  
Su kamar yayi ne  
da iska take kwashewa.   
5 Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,  
balle a sami masu zunubi a taron adalai.   
   
 
6 Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,  
amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.