Maganganun Sarki Lemuwel
31
Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya* mahaifiyarsa ta koya masa,
“Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina!
Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!
Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata,
ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.
 
“Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,
ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,
ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,
su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,
ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
bari su sha su manta da talaucinsu
kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
 
“Yi magana domin bebaye,
domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;
a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
Maganar ƙarshe. Mace Mai Halin Kirki
10  Wa yake iya samun mace mai halin kirki?
Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita
kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,
dukan kwanakin ranta.
13 Takan zaɓi ulu da lilin
ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14 Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne
tana kawo abincinta daga nesa.
15 Takan farka tun da sauran duhu;
ta tanada wa iyalinta abinci
ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;
daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;
hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
18 Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,
kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
19 Da hannunta take riƙe abin kaɗi
ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
20 Takan marabci talakawa
takan kuma taimaki masu bukata.
21 Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta;
gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
22 Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa;
tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
23 Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni
inda yakan zauna a cikin dattawan gari.
24 Takan yi riguna na lilin ta sayar;
takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
25 Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;
za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.
26 Tana magana da hikima,
kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.
27 Tana lura da sha’anin gidanta
kuma ba ta cin abincin ƙyuya.
28 ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;
haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,
29 “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo,
amma ke kin fi su duka.”
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
31 Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta,
bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.
* 31:1 Ko kuwa na Lemuwel sarkin Massa, waɗanda 31:2 Ko kuwa / amsar addu’o’ina 31:10 Ayoyi 10-31 suna bin juna layi-layi, kowace aya na farawa da harufan Ibraniyanci bi da bi.