26
Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,
haka girmamawa bai dace da wawa ba.
Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya,
haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
Bulala don doki, linzami don jaki,
sanda kuma don bayan wawaye!
Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,
in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,
in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi
haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas
haka karin magana yake a bakin wawa.
Kamar ɗaura dutse a majajjawa
haka yake da girmama wawa.
Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu
haka karin magana yake a bakin wawa.
10 Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni
haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
11 Kamar yadda kare kan koma ga amansa,
haka wawa kan maimaita wautarsa.
12 Gwamma riƙaƙƙen wawa
da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
 
13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,
zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,
haka rago yake jujjuya a gadonsa.
15 Rago kan sa hannunsa a kwano
ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
16 Rago yana gani yana da hikima
fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.
 
17 Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa
haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
 
18 Kamar yadda mahaukaci yake harbin
cukwimai ko kibiyoyi masu dafi
19 haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci
sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”
 
20 In ba itace wuta takan mutu;
haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
21 Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta,
haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
22 Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi;
sukan gangara can cikin cikin mutum.
 
23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba
haka leɓuna masu mugun zuciya.
24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,
amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,
gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,
duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;
in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,
daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.