25
Mowab sun rinjaye Isra’ila
1 Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,
2 waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.
3 Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.
4 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
5 Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”
6 Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.
7 Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi
8 ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.
9 Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.
10 Ubangiji ya ce wa Musa,
11 “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba.
12 Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi.
13 Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.”
14 Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon.
15 Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne, ’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa.
16 Ubangiji ya ce wa Musa,
17 “Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su,
18 gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”