16
Kora, Datan da Abiram
Kora ɗan Izhar, wanda yake Balawe ne daga dangin Kohatawa, wata rana ya nemi Datan da Abiram ’ya’yan Eliyab, da On ɗan Felet dukansu daga kabilar Ruben, suka haɗa kai* suka tayar wa Musa. Sai suka nemi goyon bayan sanannun shugabannin Isra’ilawa da aka naɗa a majalisa su guda 250, tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”
Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai, ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”
Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa! Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki? 10 Ya kawo ku da kuma dukan ’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist. 11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”
12 Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba! 13 Bai isa ba ne da ka fitar da mu daga ƙasar mai zub da madara da zuma, ka kawo mu nan hamada don ka kashe mu? Yanzu kuma so kake ka mai da kanka sarki a bisanmu? 14 Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!”
15 Sai Musa ya husata ƙwarai, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace wani jakinsu ba, ban kuwa cuce waninsu ba.”
16 Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can. 17 Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.” 18 Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada. 19 Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron. 20 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 21 “Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.”
22 Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan ’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?”
23 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 24 “Faɗa wa taron cewa, ‘Ku nisanci tentin Kora, da na Datan, da na Abiram.’ ”
25 Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra’ilawa kuwa suka bi shi. 26 Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.” 27 Sai suka tashi daga inda tentin Kora, da Datan, da Abiram suke. Datan da Abiram kuwa suka fita suna tsaye tare da matansu da ’ya’yansu da ’yan ƙananansu a ƙofar tentinsu.
28 Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba. 29 In waɗannan mutane sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, in abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba. 30 Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.”
31 Nan da nan da ya gama faɗi wannan, sai ƙasa ta tsage inda Datan da Abiram suke tsaye, 32 ta kuma buɗe bakinta, ta haɗiye su tare da mutanen gidansu da dukan mutanen Kora da dukan abin da yake mallakarsu. 33 Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar. 34 Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!”
35 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare.
36 Ubangiji ya ce wa Musa, 37 “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne, 38 gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.”
39 Haka Eleyazar, firist, ya tattara farantan tagulla waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo, ya ƙera murfin bagade da su, 40 yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa.
41 Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.”
42 Bayan haka, sai dukan jama’a suka taru domin su nuna rashin yardansu da abin da suke zato Musa da Haruna ne suka aikata. Da suka fuskanci Tentin Sujada, nan take sai girgije ya rufe shi, ɗaukaka Ubangiji kuwa ta bayyana. 43 Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada, 44 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki.
46 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.” 47 Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu. 48 Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya. 49 Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora. 50 Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.
* 16:1 Ko kuwa Felet, ɗauki mutane