13
Leƙen asirin ƙasar Kan’ana
(Maimaitawar Shari’a 1.19-33)
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”
3 Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.
4 Shugabannin kuwa su ne,
Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;
5 Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;
6 Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
7 Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;
8 Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;
9 daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;
10 Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;
11 Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);
12 Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;
13 Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;
14 Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;
15 Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.
16 Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)
17 Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.
18 Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.
19 Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu?
20 Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.)
21 Saboda haka suka haura, suka binciki ƙasar daga Hamadan Zin har zuwa Rehob, wajen Lebo Hamat.
22 Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)
23 Da suka iso Kwarin Eshkol, sai suka yanko reshe guda na nonon inabi tare da ’ya’yansa cunkus. Mutum biyu suka ɗauka shi rataye a sanda a kafaɗarsu, suka haɗa tare da rumman da kuma ɓaure.
24 Sai aka kira wurin Kwarin Eshkol saboda nonon inabin da suka yi cunkus, wanda Isra’ilawa suka yanko a wurin.
25 A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu.
Rahoto a kan binciken
26 Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar.
27 Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.
28 Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can.
29 Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.”
30 Sai Kaleb ya sa mutane suka yi shiru a gaban Musa, sai ya ce, “Ya kamata mu tafi mu mallaki ƙasar, gama lalle za mu iya cinta.”
31 Amma sauran mutanen da suka je tare da shi, suka ce, “Ba za mu iya kara da mutanen nan ba; sun fi mu ƙarfi.”
32 Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.
33 Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”