4
Gwajin Yesu
(Markus 1.12,13; Luka 4.1-13)
Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”
Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’*
Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’
Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’
Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”
10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’§
11 Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.
Yesu ya fara wa’azi
(Markus 1.14,15; Luka 4.14,15)
12 Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. 13 Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali 14 don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali,
da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun,
wannan yankin Galili ta Al’ummai,
16 mutanen da suke zama cikin duhu
sun ga babban haske;
haske kuma ya haskaka
a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”*
17 Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
Kiran almajirai na farko
(Markus 1.16-20; Luka 5.1-11)
18 Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne. 19 Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.” 20 Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.
21 Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su, 22 nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.
Yesu ya warkar da marasa lafiya
(Luka 6.17-19)
23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. 24 Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25 Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.
* 4:4 M Sh 8.3 4:6 Zab 91.11,12 4:7 M Sh 6.16 § 4:10 M Sh 6.13 * 4:16 Ish 9.1,2f 4:25 Wato, Birane Goma