26
An ƙulla shawara gāba da Yesu
(Markus 14.1,2; Luka 22.1,2; Yohanna 11.45-53)
1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,
2 “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,
4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
5 Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
An shafe Yesu a Betani
(Markus 14.3-9; Yohanna 12.1-8)
6 Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,
7 wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.
8 Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!
9 Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”
10 Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.
11 Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.
12 Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.
13 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
Yahuda ya yarda yă bashe Yesu
14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci
15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.
16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
Abincin yamma na Ubangiji
(Markus 14.12-21; Luka 22.7-13; Yohanna 13.21-30)
17 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18 Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”
19 Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.
21 Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22 Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
23 Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.
24 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”
25 Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?”
Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”
(Markus 14.22-26; Luka 22.14-23; 1 Korintiyawa 11.23-25)
26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.
28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Yesu ya yi maganar mūsun da Bitrus zai yi
(Markus 14.27-31; Luka 22.31-34; Yohanna 13.36-38)
31 Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa,
“ ‘Zan bugi makiyayin,
tumakin garken kuwa za su fasu.’
32 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
33 Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35 Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
Getsemane
(Markus 14.32-42; Luka 22.39-46)
36 Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.”
37 Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.
38 Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”
39 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”
40 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?
41 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
42 Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”
43 Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.
44 Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
45 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.
46 Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
An kama Yesu
(Markus 14.43-50; Luka 22.47-53; Yohanna 18.3-12)
47 Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.
48 To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.”
49 Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.
50 Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.”
Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
51 Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
52 Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.
53 Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba?
54 Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yă faru?”
55 A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagoran wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.
56 Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce-rubucen annabawa.” Sa’an nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.
A gaban majalisa
(Markus 14.53-65; Luka 22.54,55,63-71; Yohanna 18.13,14,19-24)
57 Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.
58 Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.
59 Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
60 Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.
A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61 suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”
62 Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63 Amma Yesu ya yi shiru.
Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”
64 Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”
65 Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.
66 Me kuka gani?”
Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
67 Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
68 suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu
(Markus 14.66-72; Luka 22.56-62; Yohanna 18.15-18,25-27)
69 To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”
70 Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
71 Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72 Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73 Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74 Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!”
Nan da take, sai zakara ya yi cara.
75 Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.