15
Yesu a gaban Bilatus
(Mattiyu 27.1,2,11-14; Luka 23.1-5; Yohanna 18.28-38)
1 Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
2 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”
Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
3 Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.
4 Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”
5 Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
(Mattiyu 27.15-26; Luka 23.13-25; Yohanna 18.39–19.16)
6 Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7 Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
8 Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
9 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10 Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11 Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12 Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13 Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”
Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15 Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Sojoji sun yi wa Yesu ba’a
(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)
16 Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
17 Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
18 Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”
19 Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.
20 Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
Gicciyewa
(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)
21 Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.
22 Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
23 Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.
24 Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.
25 Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
26 Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce,
Sarkin Yahudawa.
27 Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
29 Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,
30 sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”
31 Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!
32 Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
Mutuwar Yesu
(Mattiyu 27.45-56; Luka 23.44-49; Yohanna 19.28-30)
33 Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.
34 A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
35 Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”
36 Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”
37 Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
38 Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.
39 Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
40 Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.
41 A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.
Jana’izar Yesu
(Mattiyu 27.57-61; Luka 23.50-56; Yohanna 19.38-42)
42 Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43 Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44 Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.
45 Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.
46 Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.
47 Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.