13
Alamun ƙarshen zamani
(Mattiyu 24.1,2; Luka 21.5,6)
Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!”
Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”
(Mattiyu 24.3-14; Luka 21.7-19)
Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”
Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.
“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10  Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11  Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12  “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13  Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
(Mattiyu 24.15-21; Luka 21.20-24)
14  “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’*tsaye indabai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu. 15  Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. 16  Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. 17  Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 18  Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. 19  Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.
20  “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. 21  A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. 22  Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 23  Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.
(Mattiyu 24.29-31; Luka 21.25-28)
24  “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan,
“ ‘rana za tă yi duhu,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25  taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.
Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
26  “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. 27  Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.
(Mattiyu 24.32-35; Luka 21.29-33)
28  “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29  Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 30  Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. 31  Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
Ba a san rana ko sa’a ba
(Mattiyu 24.36-44)
32  “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33  Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34  Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.
35  “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36  In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. 37  Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”
* 13:14 Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11 13:14 Ko kuwa shi; haka ma a aya 29 13:25 Ish 13.10; Ish 34.4