17
Hosheya sarkin Isra’ila na ƙarshe
A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba.
Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So* sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.
Isra’ila ya tafi zaman bauta saboda zunubi
Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar. Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu. 10 Suka kafa keɓaɓɓun duwatsu da kuma ginshiƙan Ashera a kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace. 11 Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi. 12 Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.” 13  Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.”
14 Amma ba su saurare ni ba don sun kangare kamar kakanninsu, waɗanda ba su amince da Ubangiji Allahnsu ba. 15 Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.
16 Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. 17 Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.
18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari, 19 ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo. 20 Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.
21 Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi. 22 Isra’ila suka nace cikin dukan zunuban Yerobowam, ba su kuwa rabu da su ba 23 har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can.
An sāke tsugunar da Samariya
24 Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu. 25 Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane. 26 Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.”
27 Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.” 28 Saboda haka ɗaya daga cikin firistocin da aka kawo bauta daga Samariya ya dawo ya zauna a Betel, ya koya musu yadda za su yi sujada ga Ubangiji.
29 Duk da haka, jama’ar kowace ƙasa, suka ƙera tasu alloli a garuruwa masu yawa inda suke zaune, suka sa su a masujadan da mutanen Samariya suka gina a kan tuddai. 30 Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima; 31 Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim. 32 Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai. 33 Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito.
34 Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila. 35 Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya. 36 Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu. 37 Dole kullum ku mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da farillan, dokoki da umarnan da ya rubuta muku. Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada. 38 Kada ku manta da alkawarin da na ƙulla da ku, kada ku yi sujada ga waɗansu alloli. 39 Maimakon haka, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada; shi ne zai cece ku daga hannun abokan gābanku.”
40 Amma ba su saurara ba, suka nace da ayyukansu na dā. 41 Ko ma yayinda mutanen nan suke yi wa Ubangiji sujada, ba su daina bauta wa gumakansu ba. Har yă zuwa yau, ’ya’yansu da jikokinsu sun ci gaba da bin gurbin kakanninsu.
* 17:4 Ko kuwa wajen Sayis, zuwa ga; So wani mai yiwuwa gajeren suna na Osorkon. 17:12 Fit 20.4,5. 17:17 Ko kuwa Suka sa ’ya’yansu maza da mata suka ratsa