20
Biranen mafaka
(Ƙidaya 35.9-15; Maimaitawar Shari’a 19.1-13)
1 Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,
2 “Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa,
3 domin idan wani ya kashe wani bisa kuskure ba da niyyar yin kisankai ba, mutumin zai iya gudu zuwa can yă fake don kada a kashe shi.
4 Lokacin da ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen nan, sai yă tsaya a ƙofar birnin yă gaya wa dattawan wannan birni damuwarsa. Sa’an nan su karɓe shi su ba shi wurin zama a cikin birninsu.
5 In mai neman yă kashe shi don ramako ya bi shi zuwa can, ba za su miƙa shi ba domin ba da niyya ya kashe wani ba, kuma ba fushi ne ya sa ya yi kisan ba.
6 Zai zauna a wannan birni har sai taron jama’a sun yi masa shari’a, kuma har sai lokacin da babban firist wanda yake aiki a lokacin ya mutu, sa’an nan zai iya koma garinsa na dā.”
7 Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.
8 A hayin Urdun, gabas da Yeriko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ruben, Ramot cikin Gileyad a kabilar Gad, da Golan cikin Bashan a kabilar Manasse.
9 In wani mutumin Isra’ila ko kuma wani baƙon da yake zama a cikinsu, ya yi kisankai cikin kuskure, zai iya gudu zuwa biranen da aka keɓe, ba za a bari mai neman ramako yă kashe shi kafin jama’a su yi masa shari’a ba.