8
“ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura. Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa. Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
“Fada musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Sa’ad da mutane suka fāɗi, ba sa tashi ne?
Sa’ad da mutum ya kauce, ba ya dawowa?
To, me ya sa waɗannan mutane suka kauce?
Me ya sa Urushalima kullum take kaucewa?
Sun manne wa ƙarya;
suka ƙi su dawo.
Na saurara sosai,
amma ba su faɗi wata maganar kirki ba.
Ba wanda ya tuba daga muguntarsa,
sai ma cewa yake, “Me na yi?”
Kowa ta kai-ta-kai yake
kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.
Ko shamuwa ta sararin sama ma
takan san lokutan da aka tsara mata,
kurciya, mashirare da kuma zalɓe
sukan lura da lokacin ƙauransu.
Amma mutanena ba su san
abubuwan da Ubangiji yake bukata ba.
 
“ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima,
gama muna da dokar Ubangiji,”
alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda
ya yi ƙarya?
Za a kunyatar da masu hikima;
za su yi fargaba a kuma kama su.
Da yake sun ƙi maganar Ubangiji,
wace irin hikima kuka ce kuke da ita?
10 Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu
gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi.
Tun daga ƙarami har zuwa babba,
kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba;
har da annabawa da firistoci ma,
kowannensu yana ƙarya.
11 Sukan ɗaura mikin mutanena
sai ka ce mikin ba shi da matsala.
Suna cewa, “Lafiya, Lafiya,”
alhali kuwa ba lafiya.
12 Sukan ji kunyar halin banƙyamarsu kuwa?
Sam, ba su da kunya ko kaɗan;
ba su ma san yadda za su ji kunya ba.
Saboda haka sukan fāɗi tare da fāɗaɗɗu;
za su fāɗi sa’ad da aka hukunta su,
in ji Ubangiji.
 
13 “ ‘Zan ƙwace girbinsu,
in ji Ubangiji.
Ba a za sami inabi a kuringa ba.
Ba za a sami ’ya’ya a itacen ɓaure ba,
ganyayensu kuwa za su bushe.
Abin da na ba su
za a ƙwace.’ ”
 
14 Me ya sa muke zama a nan?
Mu tattaru!
Mu gudu zuwa birane masu katanga
mu mutu a can!
Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa
ya kuma ba mu ruwan dafi mu sha,
domin mun yi masa zunubi.
15 Mun sa zuciya ga salama
amma ba lafiya,
mun sa zuciya ga lokacin warkarwa
amma sai ga razana.
16 Daga Dan ana jin
tirjin dawakan abokin gāba;
da jin haniniyar ingarmunsu
dukan ƙasar ta girgiza.
Sun zo su cinye
ƙasar da kome da yake cikinta,
birni da dukan mazaunanta.
 
17 “Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku,
kāsā, waɗanda ba su da maƙari,
za su kuwa sassare ku,”
in ji Ubangiji.
 
18 Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki,
zuciyata ta ɓaci ƙwarai.
19 Ka saurari kukan mutanena
daga ƙasa mai nisa suna cewa,
Ubangiji ba ya a Sihiyona ne?
Sarkinta ba ya can ne kuma?”
 
“Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi,
da baƙin gumakansu marasa amfani?”
 
20 “Girbi ya wuce,
damuna ta ƙare,
ba a kuwa cece mu ba.”
 
21 Da yake an ragargazar da mutanena, an ragargaza ni ke nan;
na yi kuka, tsoro ya kama ni.
22 Ba magani ne a Gileyad?
Ba likita ne a can?
To, me ya sa ba warkarwa
wa raunin mutanena?