47
Saƙo game da Filistiyawa
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.
 
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa;
za su zama kogi mai rigyawa.
Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta,
garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu.
Mutane za su yi kuka;
dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
da jin motsin takawar kofatan dawakai,
da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba
da motsin ƙafafunsu.
Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba;
hannuwansu za su yi laƙwas.
Gama rana ta zo
da za a hallaka Filistiyawa
a kuma datse dukan waɗanda suka ragu
waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon.
Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa,
raguwa daga bakin tekun Kaftor.
Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki;
Ashkelon zai yi shiru.
Ya raguwar da suke zama a fili,
har yaushe za ku tsattsage kanku?
 
“Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji
sai yaushe za ka huta?
Ka koma kubenka;
ka huta, ka yi shiru.’
Amma ta yaya zai huta
sa’ad da Ubangiji ya umarta,
sa’ad da ya umarta shi
don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”