42
Sa’an nan dukan shugabannin sojoji, haɗe da Yohanan ɗan Kareya da Yezaniya* ɗan Hoshahiya, da dukan mutane daga ƙarami zuwa babba, suka zo wurin Irmiya annabi suka ce masa, “Muna roƙonka ka ji kukanmu ka kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda dukan wannan raguwar mutane. Gama kamar yadda kake gani yanzu, ko da yake dā muna da yawa, yanzu ɗan kaɗan muka rage. Ka yi addu’a cewa Ubangiji Allahnka zai faɗa mana inda za mu tafi da kuma abin da za mu yi.”
Sai Irmiya ya amsa ya ce, “Na ji ku, tabbatacce zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yadda kuka roƙa; zan faɗa muku duk abin da Ubangiji ya faɗa ba kuwa zan ɓoye muku kome ba.”
Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba. Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”
Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya. Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba. Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa, 10 ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku. 11 Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa. 12 Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’
13 “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku, 14 in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’ 15 to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can, 16 takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu. 17 Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’ 18 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’
19 “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau 20 cewa in kun yi kuskure sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’ 21 Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba. 22 Saboda haka yanzu, ku tabbatar da wannan. Za ku mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba a wurin da kuke so ku tafi ku zauna.”
* 42:1 Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma Irm 43.2) Azariya 42:20 Ko kuwa kun yi kuskure a zukatanku