37
Irmiya a kurkuku
1 Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim.
2 Shi da masu yin masa hidima da mutanen ƙasar ba su kula da maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya annabi ba.
3 Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.”
4 To, fa, Irmiya ya sami ’yancin kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a riga an sa shi a kurkuku ba.
5 Sojojin Fir’auna suka fita daga Masar, sa’ad da Babiloniyawa waɗanda suke ƙawanya wa Urushalima suka ji labari game da su, sai suka janye daga Urushalima.
6 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa,
7 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar.
8 Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’
9 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba!
10 Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.”
11 Bayan sojojin Babiloniyawa suka janye daga Urushalima saboda sojojin Fir’auna,
12 sai Irmiya ya bar birnin don yă je yankin Benyamin ya sami rabon mallaka a cikin mutane a can.
13 Amma sa’ad da ya kai Ƙofar Benyamin, sai hafsa mai tsaro, wanda ake kira Iriya ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama shi ya kuma ce, “Kana gudu daga Babiloniyawa ne!”
14 Sai Irmiya ya ce, “Ba gaskiya ba ce, ba na gudu daga Babiloniyawa.” Amma Iriya bai saurare shi ba; a maimako, ya kama Irmiya ya kawo shi wurin fadawa.
15 Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.
16 Aka sa Irmiya a can cikin kurkuku, inda ya kasance kwanaki masu yawa.
17 Sa’an nan Sarki Zedekiya ya aika a kawo shi aka kuma kawo shi fada, inda ya tambaye shi a kaɗaice ya ce, “Akwai wata magana daga Ubangiji?”
Irmiya ya amsa ya ce, “I, za a ba da kai ga sarkin Babilon.”
18 Sai Irmiya ya ce wa Sarki Zedekiya, “Wane laifi na yi maka ko fadawanka ko kuwa wannan mutane, da ka sa aka jefa ni cikin kurkuku?
19 Ina annabawanka waɗanda suka yi maka annabci suna cewa, ‘Sarkin Babilon ba zai yaƙe ka ko wannan ƙasa ba’?
20 Amma yanzu, ranka yă daɗe, sarkina, ka saurara. Bari in kawo kukata a gabanka. Kada ka mai da ni gidan Yonatan magatakarda, in ba haka zan mutu a can.”
21 Sarki Zedekiya ya yi umarni a ajiye Irmiya a sansanin matsara a kuma ba shi burodi daga titin masu gashin burodi kowace rana sai duka burodi a birnin ya ƙare. Saboda haka Irmiya ya zauna a sansanin matsara.