33
Alkawarin Maidowa
Yayinda Irmiya yana a tsare a sansanin matsara, sai maganar Ubangiji ta zo masa sau na biyu cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa. ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’ Gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da gidaje a wannan birni da fadodin Yahuda da aka rurrushe domin a yi amfani da su a kan mahaurai da kuma takobi a yaƙi da Babiloniyawa. ‘Za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata. Zan ɓoye fuskata wa wannan birni saboda dukan muguntarsu.
“ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya. Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā. Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye. Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’
10 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin 11 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa,
“ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki,
gama Ubangiji mai alheri ne;
ƙaunarsa za tă dawwama har abada.”
Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.
12 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu. 13 A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji.
14 “ ‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
15 “ ‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci
zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda;
zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar.
16 A kwanakin nan zan ceci Yahuda
Urushalima kuma za tă zauna lafiya.
Sunan da za a kira ta shi ne,
Ubangiji Adalcinmu.’
17 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba, 18 ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’ ”
19 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, 20 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba, 21 to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki. 22 Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ”
23 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, 24 “Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai* biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma. 25 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba, 26 to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’ ”
* 33:24 Ko kuwa iyalai 33:26 Ko kuwa zan komo da su daga bauta