27
Yahuda ya bauta wa Nebukadnezzar
A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda. Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan. Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.
“ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’ 10 Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka. 11 Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”
12 Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu. 13 Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba? 14 Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku. 15 ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”
16 Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne. 17 Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai? 18 In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon. 19 Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan, 20 waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima, 21 I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima, 22 ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ”