21
Allah ya ƙi amsa roƙon Zedekiya
1 Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa,
2 “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.”
3 Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa,
4 ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.
5 Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma.
6 Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba.
7 Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’
8 “Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa.
9 Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa.
10 Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’
11 “Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji;
12 Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya;
ku kuɓuta daga hannun mai danniya
wannan da aka yi wa fashi
in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta
saboda muguntar da kuka aikata
za tă ci babu wanda zai kashe ta.
13 Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima,
ku da kuke zama a bisa wannan kwari
kan dutsen da yake a fili,
in ji Ubangiji
ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu?
Wa zai iya shiga mafakarmu?”
14 Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku,
in ji Ubangiji.
Zan sa wuta a kurminku
da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ”