12
Damuwar Irmiya
1 Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji,
sa’ad da na kawo ƙara a gabanka.
Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka.
Me ya sa mugaye suke nasara?
Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?
2 Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa;
sun yi girma suna ba da ’ya’ya.
Kullum sunanka yana a bakinsu
amma kana nesa da zuciyarsu.
3 Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji;
kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai.
Ka ja su kamar tumakin da za a yanka!
Ka ware su don ranar yanka!
4 Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya
ciyawar kowane fili ta bushe?
Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne,
dabbobi da tsuntsaye sun hallaka.
Ban da haka ma, mutane suna cewa,
“Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”
Amsar Allah
5 “In ka yi tsere da mutane a ƙafa
suka kuma gajiyar da kai,
yaya za ka yi gasa da dawakai?
In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa,
ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?
6 ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka;
sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka.
Kada ka amince da su,
ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.
7 “Zan yashe gidana,
in rabu da gādona;
Zan ba da wadda nake ƙauna
a hannuwan abokan gābanta.
8 Gādona ya zama mini
kamar zaki a kurmi.
Yana mini ruri;
saboda haka na ƙi shi.
9 Ashe, gādona bai zama mini
kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama
da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba?
Tafi ka tattaro dukan namun jeji;
ka kawo su su ci.
10 Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina
su tattake gonata;
za su mai da gonata mai kyau
kango marar amfani.
11 Za tă zama kango,
busasshiya da kuma kango a gabana;
ƙasar duka za tă zama kango
domin ba wanda ya kula.
12 A kan dukan tsaunukan nan na hamada
masu hallakarwa za su zo,
gama takobin Ubangiji zai ci
daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan;
ba wanda zai zauna lafiya.
13 Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa;
za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba.
Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe
saboda zafin fushin Ubangiji.”
14 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu.
15 Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa.
16 In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata.
17 Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.