4
Fushin Yunana a kan tausayin Allah
1 Sai abin ya ɓata wa Yunana rai ƙwarai har ya yi fushi.
2 Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.
3 Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.”
4 Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?”
5 Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin.
6 Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa.
7 Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu.
8 Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
9 Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?”
Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”
10 Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita.
11 Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”