12
Yefta da Efraim
1 Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
2 Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba.
3 Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”
4 Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”
5 Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,”
6 sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.
7 Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad.
Ibzan, Elon da Abdon
8 Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.
9 Yana ’ya’ya maza talatin da ’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren ’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga ’ya’yansa maza kuwa ya kawo ’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai.
10 Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
11 Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma.
12 Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.
13 Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.
14 Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.
15 Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.