9
A gare mu an haifi yaro
1 Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.
2 Mutanen da suke tafiya cikin duhu
sun ga babban haske;
a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa
haske ya haskaka.
3 Ka fadada al’umma
ka kuma ƙara farin cikinsu;
suna farin ciki a gabanka
yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,
kamar yadda mutane sukan yi farin ciki
sa’ad da suke raba ganima.
4 Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi,
kuka ji tsoro
nauyin da ya nawaita musu,
sandar da yake a kafaɗunsu,
sandar masu zaluncinsu.
5 Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi
da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini
zai kasance an ƙone shi
zai kuma zama abin hura wuta.
6 Gama a gare mu an haifa mana yaro,
a gare mu an ba da ɗa,
gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.
Za a ce da shi
Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki
Uban Madawwami, Sarkin Salama.
7 Game da girmar gwamnatinsa da salama
babu iyaka.
Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa,
zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,
tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.
Ubangiji Maɗaukaki ne
ya yi niyyar aikata wannan duka.
Fushin Ubangiji a kan Isra’ila
8 Ubangiji ya aika da saƙon gāba da Yaƙub;
zai auka wa Isra’ila.
9 Dukan mutane za su san shi,
Efraim da mazaunan Samariya,
waɗanda suke magana da fariya
suna kuma ɗaga kai,
10 “Tubalai sun zube a ƙasa,
amma za mu sāke gina su da dutse;
an sassare itatuwan ɓaure,
amma za mu maya su da al’ul.”
11 Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su
ya kuma ingiza abokan gāba.
12 Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma
sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
13 Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba,
balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.
14 Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya,
da reshen dabino da iwa a rana guda;
15 dattawa da manyan mutane su ne kai,
annabawa waɗanda suke koyar da ƙarairayi su ne wutsiya.
16 Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su,
su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce.
17 Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba,
ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba,
gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu,
kowane baki yana faɗin mugayen maganganu.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
18 Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta;
tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya,
ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa,
don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.
19 Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki
ƙasar za tă ci wuta
mutane kuma za su zama abin hura wutar,
babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa.
20 A dama za su ci,
amma su ci gaba da jin yunwa;
a hagu za su ci,
amma ba za su ƙoshi ba.
Kowa zai mai da naman ’ya’yansa abinci.
21 Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse;
tare za su yi gāba da Yahuda.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.