65
Hukunci da kuma ceto
“Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba;
ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba.
Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba,
Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’
Dukan yini ina miƙa hannuwana
ga mutane masu tayarwa,
waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau,
suna bin tunaninsu,
mutanen da suna cin gaba da tsokanata
a fuskata,
suna miƙa hadayu a gonaki
suna ƙone turare a bagadan tubali;
suna zama a kaburbura
su kwana suna yin asirtattun ayyuka;
suna cin naman aladu,
tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta;
suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni,
gama na fi ku tsarki!’
Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina,
wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.
 
“Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa
ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa;
zan yi ramuwa a cinyoyinsu
saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,”
in ji Ubangiji.
“Gama sun ƙone turare a kan duwatsu
suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai,
zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu
cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi
mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi,
har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’
haka nan zan yi a madadin bayina;
ba zan hallaka su duka ba.
Zan fitar da zuriyar Yaƙub,
daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna;
zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su,
a can kuma bayina za su zauna.
10 Sharon zai zama wurin kiwo don shanu,
Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna,
domin mutanena da suke nemana.
 
11 “Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji
kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa,
ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a
kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara,
12 zan ƙaddara ku ga kaifin takobi,
dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka;
gama na yi kira amma ba ku amsa ba,
na yi magana amma ba ku saurara ba.
Kuka aikata mugunta a gabana
kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.”
13 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“Bayin za su ci,
amma ku za ku ji yunwa;
bayina za su sha,
amma ku za ku ji ƙishi;
bayina za su yi farin ciki
amma ku za ku sha kunya.
14 Bayina za su rera
da farin cikin zukatansu,
amma ku za ku yi kuka
daga wahalar zuciya
ku kuma yi kururuwa da karayar zuci.
15 Za ku bar sunanku
ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa;
Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku,
amma ga bayina zai ba su wani suna.
16 Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar
zai yi haka da gaskiyar Allah;
wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar
zai rantse da gaskiyar Allah.
Gama za a manta da wahalolin baya
a kuma ɓoye su daga idanuna.
Sabuwar sama da kuma sabuwar duniya
17 “Ga shi, na halicci
sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.
Abubuwa na dā za a manta da su,
ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
18 Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada
a abin da na halitta,
gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna
mutanenta kuwa abin farin ciki.
19 Zan yi farin ciki a kan Urushalima
in kuma yi murna saboda mutanena;
a can ba za a ƙara jin
karar makoki da na kuka ba.
 
20 “A cikinta ba za a ƙara jin
jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba,
ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba;
duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari
za a ce ya mutu a kurciya ne kawai;
duk wanda bai kai* ɗari ba
za a ɗauka la’antacce ne.
21 Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu;
za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu.
22 Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba,
ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba.
Gama kamar yadda kwanakin itace suke,
haka kwanakin mutanena za su kasance;
zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin
ayyukan hannuwansu.
23 Ba za su yi wahala a banza ba
ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a;
gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka,
su da zuriyarsu tare da su.
24 Kafin su yi kira zan amsa;
yayinda suke cikin magana zan ji.
25 Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare,
zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi,
amma ƙura ce za tă zama abincin maciji.
Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna
a kan dukan dutsena mai tsarki ba,”
in ji Ubangiji.
* 65:20 Ko kuwa / mai zunubin da ya kai