5
Waƙar gonar inabi 
 
1 Zan rera waƙa wa ƙaunataccena  
waƙa game da gonar inabinsa.  
Ƙaunataccena yana da gonar inabi  
a gefen tudu mai dausayi.   
2 Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun  
ya shuka mata inabi mafi kyau.  
Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta  
ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi.  
Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin,  
amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.   
   
 
3 “Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda,  
ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.   
4 Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina  
fiye da abin da na yi mata?  
Da na nemi inabi masu kyau,  
me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?   
5 Yanzu zan faɗa muku  
abin da zan yi da gonar inabina.  
Zan cire katangar da ta kewaye ta,  
za tă kuwa lalace;  
zan rushe bangonta,  
za a kuwa tattake ta.   
6 Zan mai da ita kango,  
ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba,  
sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can  
Zan umarci gizagizai  
kada su yi ruwan sama a kanta.”   
   
 
7 Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki  
ita ce gidan Isra’ila,  
mutanen Yahuda kuma  
su ne lambun farin cikinsa.  
Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini;  
yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.   
Kaito da hukunce-hukunce 
 
8 Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje  
kuke kuma haɗa gonaki da gonaki  
har babu sauran filin da ya rage  
ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.   
9 Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana,  
“Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango,  
za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.   
10 Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai,  
mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”   
   
 
11 Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe  
don su nufi wurin shaye-shaye,  
waɗanda suke raba dare  
har sai sun bugu da ruwan inabi.   
12 Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,  
ganguna da busa da ruwan inabi,  
amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,  
ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.   
13 Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta  
domin rashin fahimi;  
manyan mutanensu za su mutu da yunwa  
talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.   
14 Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa  
ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka;  
cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara  
tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.   
15 Ta haka za a ƙasƙantar da mutum  
kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam,  
za a ƙasƙanta da masu girman kai.   
16 Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya,  
kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.   
17 Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu;  
raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.   
   
 
18 Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu,  
da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,   
19 waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta,  
bari yă hanzarta aikinsa  
don mu gani.  
Bari yă iso,  
bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo,  
don mu sani.”   
   
 
20 Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta  
nagarta kuma mugunta,  
waɗanda suke mai da duhu haske  
haske kuma duhu,  
waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi  
zaƙi kuma ɗaci.   
   
 
21 Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima  
da kuma wayo a idonsu.   
   
 
22 Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi  
da gwanaye a haɗin abubuwan sha,   
23 waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,  
amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.   
24 Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara  
kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta,  
haka saiwarsu za su ruɓa  
iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura;  
gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki  
suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.   
25 Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa;  
ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su.  
Duwatsu sun jijjigu,  
gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna.  
   
 
Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba,  
bai kuwa janye hannunsa ba.   
   
 
26 Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa,  
ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya.  
Ga shi sun iso,  
da sauri da kuma gaggawa!   
27 Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe,  
babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci;  
babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi,  
ba igiyar takalmin da ta tsinke.   
28 Kibiyoyinsu masu tsini ne,  
an ɗaura dukan bakkunansu;  
kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara,  
ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.   
29 Rurinsu ya yi kamar na zaki,  
suna ruri kamar ’yan zakoki;  
suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta  
su ɗauke shi ba mai ƙwace shi.   
30 A wannan rana za su yi ta ruri a kansa  
kamar rurin teku.  
Kuma in wani ya dubi ƙasar,  
zai ga duhu da damuwa;  
haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai.